An kawar da Boko Haram daga Adamawa — Soji

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rundunar sojin ta ce Madagali shi ne gari na karshe da ke hannun Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kwato garin Madagali daga hannun 'yan Boko Haram, tana mai cewa da ma shi ne gari na karshe da ke hannun 'yan kungiyar a jihar Adamawa.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Alhamis,rundunar sojin ta ce babu sojin da ya ji rauni ko kuma ya mutu a yunkurin kwato garin.

Ta kara da cewa dakarunta na ci gaba da kakkabe gyauron 'yan kungiyar ta Boko Haram da suka rage a garin.

Jihar ta Adamawa dai na cikin jihohin da Boko Haram ta kwace wasu garuruwansu a hare-haren da take kai wa.

Kazalika, jihar na cikin uku da aka sanya wa dokar ta-baci saboda yawan hare-haren da Boko Haram din ke kai wa.