India: Amarya ta bijire wa angonta saboda bai iya lissafi ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mafi yawan auren da ake yi a Indiya iyayen mata da na mijin ne suke hadawa

'Yan sanda a India sun ce wata amarya a garin Uttar Pradesh ta bijirewa auren da za a daura mata da angonta saboda ya fadi wani gwajin lissafi da ta ba shi.

Amaryar dai ta tambayi angon nata ne idan aka tara 15 da 6 wacce amsa za a samu, yayin da shi kuma ya bata amsa da cewa 17 ke nan, sai ta tunzura ta ce ta fasa auren.

Rahotannin sun ce iyalan angon sun yi kokarin gamsar da amaryar ta dawo a daura auren, amma sai ta ki hakan, tana mai cewa ba shi da ilmi.

'Yan sanda a garin sun ce sun yi kokarin sasanta tsakanin iyalan amma hakan ya ci tura, inda dukkan bangarorin suka mayar wa juna kayayyakin da suka karba kafin auren.

An ruwaito baban amaryar Mohar Singh yana cewa "Iyalan angon ne suka munafunce mu tare da barin mu a duhu a kan rashin ilmin dansu."

"ko da dan firamare zai iya amsa wannan tambaya ta sassaukan lissafi". In ji baban amaryar.

A watan jiya ne aka sami irin wannan lamarin inda wata amarya a garin Uttar Pradesh ta bijire wa angonta a wajen daurin auren ta, ta auri daya daga cikin bakin da suka hallarci taron bayan da ciwon farfadiya ya kama shi gabanin daurin auren.