Sojin Nigeria ba su kwato Bama ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar sojin Nigeria ta musanta ikirarin Namadi Sambo cewa sun kwato ikon garin Bama

Rahotanni daga Najeriya na cewa har yanzu dakarun tsaron Najeriya ba su kai ga kwato garin Bama ba, sabanin ikirarin da mataimakin shugaban Najeriya Namadi Sambo ya yi a hirarsa da BBC cewa sojojin Najeriyar sun kwato garin.

Wasu majiyoyi na tsaro sun tabbatar wa da BBC cewa ana kokarin karbo garin na Bama ne a yanzu, amma ba a kai ga kwato garin ba.

Majiyoyin tsaron sun shaida wa BBC cewa, ya zama dole su fito su bayyana hakan ne don kaucewa illar da hakan ka iya yi ga wasu fararen hula da ka iya nikar gari su tafi garin.

Don haka suka ce kada farar hular da ya tunkari garin tukunna har sai hukumomin tsaro sun bada tabbacin za a iya komawa garin.