Guguwa ta afkawa tsibirin Vanuatu

Ana kwashe kankarar da mahaukaciyar guguwa ta haddasa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

mahaukaciyar guguwar ta daidaita tsibirin

Wata mahaukaciyar guguwa na can tana wujijjiga tsibirin Vanuatu a wani abinda Majalisar Dinkin Duniya tace yanayi na iskar da ba a taba gani ba a tarihin yankin Pacific.

Ana fargabar mutanen da za ta hallaka suna da matukar yawa.

Mahaukaciyar guguwar da aka yi ma lakani da Pam tana juyawa ne da wata irin iska mai tafiyar kilomita dari 2 da hamsin a cikin sa'a guda tare da ruwan sama mai karfi da toroko na teku.

Ta kwashe rufi na gidaje tare da tumbuke itatuwa da yanke wutar lantarki da hanyoyin samun ruwan sha.

Hanyoyin sadarwa sun yanke, za a kuma dauki kwanaki da dama kafin a tantance yawan barnar da ta yi a wasu yankuna na tsibirin.