WHO: Ebola ta hallaka mutane sama da 10,000 a Afrika

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumar lafiya ta duniya tace akwai bukatar tashi tsaye don kawar da annobar dungurugum.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ya zuwa yanzu annobar cutar Ebola da ta barke a yammacin Afrika ta hallaka mutane sama da 10,000 a kasashe uku da cutar ta fi kamari.

Hukumar tace yakin da ake yi da cutar yana tafiya yadda ya kamata, amma kuma ta yi gargadin cewa akwai bukatar kara tashi tsaye don kawar da annobar da duniya ba ta taba shaida kamar ta ba.

Za a kwantar da wani ma'aikacin lafiya na Amurka da ya kamu da cutar a Saliyo a wata cibiya ta musamman dake Maryland bayan an mayar da shi kasar ta Amurka.

Akwai kuma wani ma'aikacin lafiyar dan Biritaniyar da ya kamu da cutar a Saliyo wanda shi ma aka kwasa zuwa wata cibiya dake London.

Annobar cutar ebola dai ta bullo ne daga kasar Guinea in da ta yadu zuwa Liberiya da Saliyo, an kuma samu bullarta a Nigeria da Mali amma ba ta yi kamari ba.