Sabbin iraruwa don manoman Afrika

Sabbin iraruwan shuka don manoman Afrika Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Sabbin iraruwan shuka don manoman Afrika

An kaddamar da wani shiri na taimakon kananan manoma samun iraruwan shuka na zamani masu samar da yabanya.

Cibiyar TASAI wadda ta bullo da tsarin na samar da iraruwan ta yi nazarin halin da wannan sashe na iraruwan da manoman Afrika ke shukawa tare da nuna irin matsalolin dake hana iraruwa kaiwa ga manoma.

Masu wannan shiri suna fata wannan tsari zai yi tankade da rauraya ga shekarun da aka shafe gwamnati na murda wannan sashe na samar da iraruwan shuka.

Kasashen Uganda da Zimbabwe da Afrika ta Kudu da Kenya ne aka fara nazari a wannan tsari.

Edward Mabaya babban jami'in bincike na Cibiyar ta TASAI ya ce wadatar abinci shine babban burin da ake da shi ga aikin gona a Afrika wadda mafi rinjayen manoman ta masu karamin karfi ne.

A al'ada, gwamnati ce ta mamaye wannan fanni na samar da iraruwan shuka ga manoma a shekarun 1970 da 1980, to amma yace, an samu sauyi a shekarun 1990.

Yawancin wannan tsarin an kawar da shi, wannan ma shine abinda ya kawo shigowar kamfanoni masu samar da iraruwan shuka na ciki da wajen nahiyar.

To amma wannan sauyi da aka samu ya haddasa fuskantar kalubale da dama kamar su yadda za a tabbatar da wadatar da iraruwan ta hanyoyin da aka tsara da kuma fasahar da yakamata kananan manoman su yi amfani da ita a wurin shuka.

Dr Mabaya ya gaya ma sashen labarai na BBC cewar "mun yi tunani cewar muna bukatar wata hanya da za ta bayar da damar tafiyar da gwaji cikin hanzari a wannan fanni ta yadda masu ruwa da tsaki kamar masu yanke shawarwari da masu zuba jari za su yi aiki da ita.

Hanyar isar da iraruwan har yanzu tana da tattare da mishkila, don haka idan akwai wani wanda ke wannan fanni da ba ya aiki yadda yakamata, ko kuma akwai abinda ke kawo cikas, to iraruwan ba za su samu kaiwa ga kananan manoma ba."

Karin bayani