An sace 'yan kasar China a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mastalar sace mutane 'yan kasar waje ta fi kamari a kudancin Najeriya

Rundunar 'yan sanda a jihar kogi da ke tsakiyar Najeriya ta tabbatar da sace wasu ma'aikata 'yan kasar China uku a Lokoja.

Mr. Samuel Adeyemi Ogunjemilusi ya tabbatarwa da BBC sace ma'aikatan 'yan kasar China uku.

Sai dai baya ga hakan ba yi wani karin bayani ba dangane da halin da ake ciki a yanzu ba.

Wasu 'yan bindiga ne dai da ba a san ko su wanene ba suka yi awon gaba da 'yan kasar China a ranar Juma'a.

Lamarin da ya yi sandiyyar mutuwar wani dan sanda guda, yayin da wani dan sandan kuma ya samu raunuka.

Jihar ta Kogi dai tana fuskantar sace mutane 'yan kasashen waje tare da neman kudin fansa, matsalar da a da tafi kamari a kudancin Najeriya.

A makon jiya ne aka sako wata Ba Amurkiya da aka sace a wata makarantar kiristoci da ke kauyen Emiworo da ke jiahar ta Kogi.