An sako 'yan China da aka sace a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan sanda a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya sun ce an sako ma'aikatan nan uku 'yan kasar China wadanda aka sace ranar Juma'a.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Samuel Adeyemi Ogunjemilusi, ya tabbatar da sakin mutanen.

Ba a sani ba ko an biya kudin fansa kafin a sako su ko kuwa a'a.

Dan sanda daya ya rasa ransa wani kuma ya sami raunuka yayin musayar wuta lokacin da 'yan bindigar da suka yi garkuwa da mutanen suka far ma wurin da 'yan Chinan ke aiki a wani wurin fasa dutse da ke wajen Lokoja, babban birnin jihar.

An sami yawaitar garkuwa da mutane musamman ma 'yan kasashen waje a jihar Kogin a bana.

A makonni biyun da suka wuce an yi garkuwa da wasu 'yan China biyu da kuma wata 'yar Amurka ma'aikaciyar mishin wadda aka yi awon gaba da ita daga makarantarta. Sai bayan mako guda aka sako ta.

Karin bayani