NLC ta Nigeria ta zabi sabon shugaba

Image caption Kungiyar ta kuma zabi sabbin shugabanni a lokacin zaben

Babbar kungiyar kwadago a Najeriya ta NLC ta zabi Comrade Ayuba Wabba a matsayin sabon shugabanta.

A ranar Asabar kungiyar ta bayar da sanarwar cewa Wabba ya lashe zaben da kungiyar ta yi na kasa a birnin Abuja.

Comrade Wabba zai shafe shekaru hudu masu zuwa yana rike da mukamin shugabancin kungiyar NLC.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa abokin hamayyarsa, Comrade Joe Ajero, na kalubalantar sakamakon zaben.

Bisa zargin cewa an yi magudi a yayin zaben.

Kungiyar NLC gamayya ce ta kungiyoyin kwadago da dama kuma tana da tasiri a kan al'amuran kasar, musamman wanda ya shafi ma'aikatan gwamnati.