Boko Haram: Sojin Nigeria za su yi taro

Dakarun sojin Nigeria
Image caption Sojojin Nigeria dai na ci gaba da yaki dan kawo karshen mayakan Boko Haram.

A Najeriya, a ranar Litinin ne rudunar sojan kasar za ta gudanar da wani babban taro na manyan jami'anta a Abuja babban birnin kasar.

Ana sa ran mahalarta taron za su tattauna ne a kan aikace-aikacen rundunar sojan kasar, tare kuma da yin bita a kan yakin da sojojin kasar ke yi da mayakan kungiyar Boko Haram.

Haka kuma taron zai duba shirye-shiryen da ake yi ta fuskar tsaro gabanin da kuma bayan zabukan kasar.

Mahalarta taron za su duba ko ana gudanar da ayyukan soji yadda ya kamata ko ba a yi.

Kazalika za a duba makomar sojojin kasa na Nigeria nan da shekaru 20.