Ana ci gaba da gwabza fada a Libya

'Yan tawaye a Libya
Image caption Kasar ta shiga tsaka mai wuya tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Mu'ammar Gaddafi.

Ana gwabza kazamin fada a Libya tsakanin kungiyoyin kawance na sojin sa kai daga yammacin kasar da magoya bayan kungiyar nan dake gwagwarmayar kafa daular Musulunci. Sun gwabza fadan a wajen birnin Sirte na tsakiyar kasar - wanda shine mahaifar hambararren Shugaban kasar ta Libya Mua'ammar Gaddafi.

Masu jihadin dake da alaka da kungiyar dake fafutukar kafa daular ta Musulunci sun kwaci gine-ginen gwamnati da gidan radiyo na jihar a birnin cikin watan jiya, a wani yunkuri na fadada hare-haren da suke kaiwa a Libya.

Kasar ta Libya dai ta tsunduma cikin rudani tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Kanar Mu'ammar Gaddafi ya yin da kawancen kungiyoyin sojin sa kai a gabashi da yammacin kasar ke gwagwarmayar kwatar iko da sassan kasar da albarkatunsu.