Za a dade ba a sasanta ba kan dumamar yanayi

Hayaki mai dumama duniya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hayaki mai dumama duniya

Babban wakilin Amurka a shawarwarin da ake yi game da muhalli ya yi gargadin cewa za a yi takaddama sosai kafin a cimma matsaya kan batun rage hayakin dake kawo dumamar yanayi.

Todd Stern ya shaida ma BBC cewar zuwa karshen wannan watan, yana sa ran Amurka za ta yi shela game da babban kudurin da take da shi a kan sauyin yanayi.

Ya yaba ma China bisa ga tayin da ta gabatar a taron kolin da za a yi kan batun yanayin cikin watan Disamba a birnin Paris.

To amma yace taron kansa ba zai warware matsalar sauyin yanayi ba. Ya yi tankiya cewar za a kwashe shekaru da dama ana wannan kokari.

Kasashe sun kagara a gudanar da taron na Paris domin kauce ma nanata taron ban-kunyar da aka yi a Copenhagen a shekara ta 2009 wanda ya gaza cimma matsaya ta ceton duniyar.

A wannan karon, kasashe masu arziki sun amince su gabatar da tayi gabanin taron don rage yiwuwar samun yamutsi a taron.

Tarayyar Turai ta rigaya ta gabatar da tayin rage kashi 40 cikin dari na hayakin da kasashen kungiyar ke fitarwa a shekara ta 1990 zuwa shekara ta 2030. Nan ba da jimawa ba Amurka za ta ba da tayin mai yiwuwa rage kashi 26 zuwa kashi 28 cikin dari na hayakin da take fitarwa zuwa shekara ta 2025.

Da wuya dai a iya kwatantawa saboda kowacce kasa, mizanin kudurin ta ya bambanta, to amma wasu kwararru sun ce za a iya kwatanta Tarayyar Turan da Amurka ta hanyar la'akri da kokarin da suke yi.

Ana sa ran China za ta yi tayin rage hayakin da take fitarwa zuwa shekara ta 2030, sannan kuma ta samar da kashi 20 cikin dari na bukatun makamashin ta daga nukiliya da wasu hanyoyin na dabam a wannan ranar da ta tsayar.

Mr Stern yace "za ka iya duba Amurka, Trayyar Turai da China - za ka ce , ina ma dai za su yi kuduri fiye da wanda suka yi, to amma wannan shine burin China. Kodayake dai babu tabbas, sai dai kuma wane ne yake da tabbas."

Karin bayani