Guguwar Pam ta yi kaca-kaca da Vanuatu

Vanuatu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Guguwar ta lalata dukkan ayyukan ci gaba da ke Vanuatu.

Shugaban kasar Vanuatu Baldwin Lons-dale ya ce mahaukaciyar guguwar da ta yi kaca-kaca da tsibirin Pacific a ranar Juma'a, yanzu ta shafe dukkan wani ci gaba, yana mai cewa dole ne kasar ta sake komawa tun farko.

Lokacinda yake magana daga kasar Japan, wurin da yake halartar wani taro, ya bayyana mahaukaciyar guguwar a matsayin wata babbar dodanniya.

Wani wakilin BBC wanda bai dade da isa babban birnin kasar, Port Vila ba ya ce guguwar ta rusa kusan kowanne gini.

Wasu mazauna Port Vila sun shaida wa BBC cewa guguwar ta lalata gidajensu, suna masu cewa yanzu ba su da komai kuma ba su taba ganin guguwa irin wannan ba.

Kawo yanzu dai adadin da ake da shi na mutanen da suka mutu kadan ne.

Har yanzu yawancin hanyoyin sadarwa ba su aiki, kuma akwai fargabar cewa za a samu karuwar mutanen da suka rasa rayukansu a wasu tsibirai da aka gaza kai wa gare su.