An kwance bama-bamai a sansanin Yarwa

Wasu 'yan gudun hijira a Nigeria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dubban mutane sun tsere daga muhallinsu sakamakon rikicin Boko Haram.

A jihar Borno dake arewacin Najeriya, jami'an tsaro sun kwance wasu bama-bamai da aka dasa a sansanin 'yan gudun hijira na Yarwa dake garin Maiduguri.

Wasu 'yan gudun hijira dake sansanin sun shaidawa BBC cewa wasu daga cikin su ne suka binne bama-baman a sansanin, amma dubun su ta cika.

Mutanen da aka kama din sun yo gudun hijira ne daga garin Bama na jihar ta Borno, inda aka nada su mukamin 'yan kato da gora wato Civilian JTF da za su kula da 'yan gudun hijirar da ke cikin sansanin na Yarwa.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar NEMA ta tabbatar da kwance bama-baman, kuma ta ce babu wani da ya rasa ransa ko ya samu rauni a lamarin.