Sojin Nigeria sun kwato garin Bama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Nigeria sun kwato wasu garuruwa daga hannun 'yan Boko Haram

Rahotanni daga Nigeria na cewa sojojin kasar sun kwato garin Bama a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar daga kungiyar Boko Haram.

Sojojin sun samu nasarar kwato garin ne bayan sun yi artabu da mayakan kungiyar ta Boko Haram a ranar Litinin.

Kakakin hedikwatar tsaro ta Nigeria, Manjo Janar Chris Olukolade ne ya tabbatarwa BBC lamarin.

Hakan dai na zuwa ne bayan da rundunar sojojin Najeriyar ta ce ta samu nasarar kwato garuruwa da dama daga hannun 'yan Boko Haram din da suka hada da garin Baga.

Tun a watan Satumbar 2014 ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kwace ikon garin Bama.

Bayanai sun nuna cewa garuruwan Gwoza da Damasak ne manyan garuruwan da suka rage sojin Najeriya ke kokarin kwatowa daga hannun Boko Haram.