Yadda ake gano yanar ido ta wayar salula

Image caption Yanar Ido na makantar da jama'a

A kasashen yammacin duniya, yin tiyata don cire yanar ido abu ne da ake yi akai-akai. Amma a Afrika, yana yi wa mutane matukar wahala su samu damar da za a binciki lafiyar idanunsu tare da magance halin da suke ciki, kuma hakan na iya yi wa rayuwarsu illa.

Kauyen Kotyana shi ne garinsu Ndawayipheli mai shekaru 72 da matarsa Nojongile mai shekaru 68.

Kauye ne mai matukar kyau mai nisan fiye da kilomita 1,300 daga Cape Town, babban birnin Afrika ta Kudu.

Haka kuma in ba a baya-bayan nan ba, ma'auratan ba sa samun dama da annashuwar kallon fuskokin juna saboda zamantowarsu makafi.

Ma'auratan dai Nojongile da Ndawayipheli, sun makance ne sakamakon matsalar yanar ido, lamarin da za a iya maganceshi cikin mintuna 20 ta hanyar yin tiyata, amma a garesu kai wa ga inda za a binciki lafiyarsu da basu magani na da matukar wahala saboda surkukin kauyen da suke zaune.

Image caption Ana gwada lafiyar idon Ndawayipheli

Sai dai a baya-bayan nan ne aka samar da yin tiyatar cire yanar ido a wani waje da bai wuce nisan sa'a daya ba daga Kotyana, inda a nan ne aka yi wa Nojongile da Ndawayipheli tiyata a farkon shekarar nan.

'Samar da dama'

Matsalar da mazauna karkara suke samu kan irin wadannan matsaloli ne ya zaburar da Dakta William Mapham, wani babban Likitan ido a asibitin Tygerberg.

Ya kirkiro da wata manhaja da ake amfani da ita a kan manyan wayoyi na zamani, mai suna manhajar Vula.

Vula na nufin 'bude wa' a harshen Siswati da Xhosa da kuma Zulu, kuma manhajar za ta baiwa ma'aikatan lafiya ako ina a kasar damar tantance masu lalurar ido a kauyuka, inda za su hadasu da kwararru a harkar idanu.

'Dawo da gani'

A sakamakon tiyatar da aka yi domin cire mata yanar ido, yanzu Nojongile tana iya gani da idanunta tana kuma yin ayyukanta na gida.

Duk da nasarar da aka samu na aikin idon da aka yi wa matarsa Nojongile, har yanzu Ndawayipheli yana dari-dari wajen yarda a yi masa aiki.

Nojongile dai tana iyaka bakin kokarinta don gamsar da mijinta ya amince a yi masa aikin.

Amma daga bisani ya yarda a yi masa tiyata.

Image caption Asibitin da Dr William Mapham ya kirkiri manhajar

Ga Likitoci da yawa da ke kauyuka, suna fuskantar kalubale wajen magance matsalar ido saboda su ba kwararru bane a harkar idanu.

Don haka sun yi maraba kwarai da samun damar da nan take za ta sadasu da kwararru a harkar idanu, wadda hakan za ta sauya yanayin aikinsu.

Med in Africa wani shiri ne na musamman kan lafiya a Afrika da BBC ta shirya.