Yunkurin hana bakin haure shiga Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban 'yan cirani ne ke rasa rayukansu a kokarin tsallake Mediterranean Sea domin shiga Turai

Hukumar 'yan sandan Turai, Europol, ta kaddamar da wani shiri na kawar da gungun masu taimaka wa bakin haure tsallaka Bahar Rum (Mediterranean Sea) domin shiga Turai.

Europol ta ce wani sabon sashe na hukumar zai yi aiki kafada da kafada da hukumar kula da iyakoki ta tarayyar Turai da kuma kasashen da ke karkashin kungiyar domin yin ayyukan leken asiri kan mutanen da ke taimaka wa bakin haure shiga nahiyar Turan.

Dubun-dubatar 'yan cirani ne ke rububin tsallake Bahar Rum a kowacce shekara.

A shekara ta 2014 ne kuma fiye da mutane 3,000 suka halaka a cikin tekun naBahar Rum a hanyarsu ta shiga nahiyar Turai.

'Yan ciranin dai na tahowa ne daga nahiyar Afrika a kokarinsu na samun ingantacciyar rayuwa a Turai, saboda matsalolin yake-yake da talauci da suka addabi kasashensu.