Ghali Na'Abba ya koma jam'iyyar APC

Hakkin mallakar hoto nass
Image caption Alhaji Ghali Na'Abba ya zargin jam'iyyar PDP

Tsohon shugaban majalisar wakilan Nigeria, Ghali Umar Na'Abba ya koma jam'iyyar APC kwanaki biyu bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Na'Abba ya ce ya koma APC ne saboda ana bukatar canji kuma jam'iyyar PDP ba ta bin tsarin demokradiyya.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif John Oyegun ne ya karbi Ghali Na'Abba a cikin jam'iyyar a shalkwatar APC da ke Abuja.

A shekara ta 2005 ne Na'Abba ya bar PDP ya koma jam'iyyar adawa ta AC kafin ya kara koma wa PDP a shekara ta 2007.

Jam'iyyar PDP na fuskantar kalubale mai girma a yayinda ake fuskantar zabukan kasar a karshen wannan watan.