Ana ci mana tuwo a kwarya lokacin zabe-Nakasassu

Image caption Manyan zabuka a Najeriya na kara karatowa

A Najeriya, masu larurar nakasa sun koka kan yarda wasu mutane suke zaba musu jam'iyyar da ba ita suke so ba lokacin zabe.

Wasu masu larurar da suka hada da kutare da makafi da guragu da dai sauransu a jihar Edo sun shaida wa BBC cewa duk lokacin da masu irin wadannan larura suka nemi a yi musu jagora don yin zabe sai a zaba musu abin da ba shi suke so ba.

Sai dai kuma hukumar zaben kasar ta ce tayi shirin share wa masu irin wannan larura hawaye.

Hukumar ta ce ta horas da jami'anta domin ba wa nakasassu da gajiyayyu da ma tsofaffi taimakon na musamman yayin kada kuri'a.