Ba zan yarda Palestine ta samu 'yancin kai ba-Netanyahu

Hakkin mallakar hoto v
Image caption Firaiministan Isra'ila, Benyamin Natenyahu

Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ci alwashin cewa ba zai yarda a ayyana Palesdinu a matsayin kasa mai-cin gashin kanta ba idan dai har ya samu nasarar sake zama firaiminista.

Mista Netanyahu ya bayyana hakan ne a matsayin wani batu da yake yin kamfe da shi don janyo hankalin al'ummar kasar su zabi jam'iyyarsa ta Lukid Party a zaben majalisar dokoki da kasar take gudanarwa a ranar Talata.

Netanyahu ya ce mika wa Palasdinawa wani yankin kasar Isra'ila tamkar bai wa musulmai dama su yaki kasar ne.

Hakan a fahimtar jam'iyyar adawa ta Zionist Union wani yunkuri ne na neman boye badakalar dake addabar kasar musamman yanayin tsadar rayuwa da kasar take fuskanta a halin yanzu.

Jam'iyyar ta yi alkawarin kyautata dangantakar kasar ta Isra'ila da Palasdinawa da kuma sauran kasashen duniya.