2015: Soji ba za su je rumfunan zabe ba — Jega

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Ana nuna damuwa game da batun tsaro a rumfunan zabe a Nigeria

A yayin da ya rage kasa da makonni biyu a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, hukumar zaben kasar ta kore yiwuwar amfani da jami'an soji a rumfunan zabe.

A wajen wani taron tattaunawa tare da jama'a a Abuja babban birnin Nigeria, Shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Attahiru Jega, ya ce hukumar ba ta taba yin amfani da sojoji a rumfunan zabe ba, kuma a wannan karo ma, ba za ta yi hakan ba.

Batun ko za a yi amfani da sojoji a zabukan da ke tafe a Najeriyar dai, ya haifar da cece-kuce a tsakanin jama'ar kasar.

Sai dai wasu masu lura da al'amuran tsaro sun bukaci hukumar ta duba lamarin da kyau domin gujewa duk wani tashin hankali da wasu magoya bayan 'yan siyasa za su iya haddasawa a rumfunan zaben.

Za a gudanar da zaben 2015 a Nigeria karkashin wani yanayi na damuwa game da sha'anin tsaro.