Jonathan ya rantsar da sabbin ministoci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Jonathan na shirin fuskantar zabe a karshen watan Maris

Shugaba Goodluck Jonathan ya rantsar da sabbin ministoci takwas da majalisar dattijai ta tantance.

Jim kadan bayan rantsar da ministocin kuma, Mr Jonathan sanar da ma'aikatun da ministocin za su jagoranta.

An nada Sanata Patricia Akwashiki, a matsayin ministar yada labarai da Farfesa Nicholas Ada, karamin minista na daya a ma'aikatar harkokin waje sai kuma Sanata Musiliu Obanikoro karamin minista na biyu.

Kanar Augustine Akobundu shi aka nada karamin minista a ma'aikatar tsaro, yayin da Mr. Fidelis Nwankwo ya kasance karamin minista a ma'aikatar lafiya.

Ita kuwa Mrs. Hauwa Bappa ta zama minista a ma'aikatar harkokin Niger Delta sai kuma Mr. Kenneth Kobani wanda aka nada minista a ma'aikatar cinikayya. Shi kuwa Sanata Joel Ikeya an nada shi ne ministan kwadago.

Sannan shugaba Jonathan ya tabbatar da Khalliru Alhassan, a matsayin Ministan Lafiya bayan shafe watanni a matsayin mai kula da ma'aikatar tun lokacin da Farfesa Onyebuchi Ckukwu ya yi murabus.