Senegal na so a rage wa'adin mulkin shugabanni

Image caption Shugabannin Afirka na son dorewa akan mulki

Shugaban Kasar Senegal Macky Sall, yace zai gudanar da kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a a badi, a kan ko ya kamata a rage wa'adin mulkin shugaban kasa daga shekaru bakwai zuwa biyar.

Mr Sall ya ce yana son ya nuna wa duniya cewa 'yan Afirka, na iya bayar da misali, kuma mulki ba shi ne dukkan jin dadin rayuwa ba.

Shugabannin kasashen Afirka da dama sun yi yunkurin tsawaita wa'adinsu a ofis a 'yan watannin nan.

Mr Sall dai ya hau kujerar mulkin kasar ne bayan wata gagarumar zanga-zangar nuna kin jinin yunkurin da tsohon shugaba Abdulaye Wad na kasar ya yi, na canza kundin tsarin mulkin kasar, ta yadda zai samu damar tsayawa takara a wa'adi na Uku.