Nigeria: An rage kudin wutar lantarki

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Nigeria na fama da karancin wutar lantarki.

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta bayar da sanarwar rage kudin wutar lantarki da kashi 50 cikin 100.

Hukumar da ke sa ido a kan lamuran wutar lantarki, NERC, ta ce hakan ya zo ne bayan da korafe-korafe suka yi yawa, musamman daga kungiyar masu masana'antu ta kasa a kan tashin gwauron zabin da kudin lantarkin ya yi, lamarin da ta ce yana yin babbar illa ga kasuwanci da masana'antu.

Dokar da ta yi garambawul ga bangaren samar da wutar lantarki da kuma kundin ka'idojin hukumar NERC sun bai wa hukumar hurumin sauya shawara a kan duk wani mataki da ta dauka idan wadanda abin ya shafa suka yi koke a cikin kwanaki 60 da yanke shawarar.

Da yake karin haske game da rage kudin, shugaban hukumar da ke kula da kamfanonin samar da wutar lantarki ta kasa, Sam Amadi, ya ce wannan ragin zai fara aiki ne a karshen watan Maris.

"Gwamnati ta bi matakin rage kudin ne bayan ta tuntubi masu ruwa da tsaki a harkokin wutar lantarki sakamakon koke-koken da jama'a suka gabatar wa hukumar a kan tsadar wutar alhalin kuma ba a samun wutar a-kai-a-kai," inji Mista Amadi.

A daya bangaren kuma hukumar ta ce an bai wa kamfanonin da ke rarraba wutar lantarki umarnin yanke wutar duk wadanda ba su biya basussukan da ake binsu ba.