Wali: Za mu bincika takaddamarmu da Morocco

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaba Jonathan ya bayar da umarnin bincike a kan takaddamar Nigeria da Morocco.

Ministan harkokin wajen Nigeria Ambasada Aminu Wali, yace ya dukufa ga binciken asalin sanarwar nan da ma'aikatarsa ta fitar, da ke cewa Shugaba Jonathan ya tattauna da Sarkin Morocco ta waya, wadda ta haddasa wata takaddamar diplomasiyya tsakanin kasashen guda biyu.

Ambasada Aminu Wali ya amsa cewa lallai wannan sanarwar daga ma'aikatarsa ta fito.

"Shugaban kasa ya yi min magana a kan cewa bai ji dadin abin da ya faru ba, kuma ya bani umarni in yi bincike in ga yaya akayi aka samu wannan matsala," a cewar Ministan.

Ya kara da cewa a kan samu kuskure irin wannan a harkar diplomasiyya, "amma tun da an saka siyasa a cikin namu sh iyasa a ka mai dashi wani abu daban," inji Aminu Wali.

A makon jiya ne dai kasar Maroko ta kira jakadanta gida daga Nigeria, bayan ma'aikatar harkokin wajen Nigeria ta fitar da sanarwar, wadda ta ce Sarkin kasar ta Morocco ya yi wata hira ta waya da shugaba Goodluck Jonathan, duk da musanta hakan da masarautar Moroccon ta yi.

Daga bisani fadar shugaban Nigeriar ta musanta batun tattaunawar.