An gano guba a fadar gwamnatin Amurka

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wannan ba shi ne karon farko da ake samun barazanar tsaro a fadar ba

Hukumar leken asirin Amurka tace tana gudanar da karin gwaje gwaje akan wata takaddar abulan da aka aika zuwa fadar white house wacce ka iya zama tana dauke da guba.

Gwaje gwajen farko ya nuna cewa tabbas takaddar anbulan din na dauke da guba.

Hukumar leken asirin Amurkar wacce tsaron lafiyar Shugaba Obama ya rataya a kanta, ta ce ana gudanar da bincike yanzu.

Hukumar ta kuma ce ba zata kara cewa komai ba