"Man da ya malala a Nigeria ya wuce kima"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Amnesty International ta ce man da ya malala a Najeriya ya wuce kima

Kungiyar kare hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta ce malalar man da manyan kamfanonin mai biyu suka haddasa a Najeriya ta kai a ayyana lamarin a matsayin dokar ta-baci da a wasu kasashen ne.

Amnesty ta ce kamfanin Shell da na ENI sun haddasa malalar mai sau 550 a shekarar 2014.

Ta kara da cewa ikirarin da kamfanonin suka yi cewa litar ma miliyan biyar ce ta malala sanadiyar ayyukansu na hakar man ba gaskiya ba ne, tana mai cewa adadin ya zarta hakan.

Kamfanonin man dai sun dora alhakin yawancin malalar man ne bisa ayyuakan masu satar mai, wadanda ke sayar da man a kasuwanin bayan-fage.