Ba zan koma PDP ba — Atiku

Image caption Atiku Abubakar ya ce har adaba ba zai komai PDP ba

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce ba zai fita daga jam'iyyar APC ba.

Alhaji Atiku ya tabbatarwa BBC cewa shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya ziyarce shi, inda ya bukace shi ya koma jam'iyyar PDP, amma ya gaya masa ba zai taba komawa jam'iyyar ba.

Kazalika Alhaji Atiku Abubakar ya nisanta kansa daga wasu kungiyoyi da suka ce magoya bayansa ne, wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar ta APC zuwa PDP a farkon makon nan.

A cewarsa bai san 'yan kungiyoyin ba, kuma ma ba shi da wata dangantaka da su.

Ziyarar da shugaba Jonathan ya kai wa tsohon mataimakin shugaban kasar dai ta janyo cece-kuce a kasar, lamarin da ya sa wasu ke zargi yana son komawa jam'iyyar PDP ne.