'Yan Boko Haram sun kashe mata a Bama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kashe matan da suka aura dole a garin Bama kafin sojoji su sake kwace garin.

Bayanai sun nuna cewa matan su sittin sun gamu da ajalinsu ne saboda sun ki yarda su bar garin tare da 'yan Boko Haram din a lokacin da 'yan kungiyar suka samu labarin cewa sojoji za su shiga garin.

A ranar Litinin din da ya gabata ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da kwace garin na Bama bayan ya kwashe kusan watanni bakwai a karkashin ikon Boko Haram.

Wani mutum wanda ya ziyarci matan da suka tsere daga garin Bama kuma wadanda suka zo da labarin ya tabbatar da BBC afkuwar lamarin.

"Sun kashe mata kusan 60 da suka ki yarda su bisu a ranar Lahadi da ta wuce," in ji mutumin.

Dakarun Najeriya tare da hadin gwiwar na Chadi da Kamaru da kuma Nijar sun kaddamar da yaki a kan Boko Haram inda bisa dukan alamu a yanzu suke samun nasara a kan mayakan.