Ango Abdullahi ya tsallake rijiya da baya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojoji sun bude wa motar shugaban kungiyar dattawan arewa wuta a Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi a Nijeriya na cewa wasu sojoji sun bude wuta a kan shugaban kungiyar dattawan arewacin kasar, Northern Elders Forum, Farfesa Ango Abdullahi, yayin da yake tafiya a mota tare da wasu na hannun damarsa.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, yayin da yake kokarin fita daga birnin Bauchi, amma dai ya tsallake rijiya da baya, kuma bai yi ko kwarzane.

Farfesa Abdullahi ya shaida wa BBC cewa motar tasu tana tafiya ne a hankali ba tare da aikatawa wani ganganci ba lokacin da sojojin suka bude musu wuta.

"Mun ga mota pick-up da sojoji a gabanmu, kuma mun ga motoci suna wuceta, to sai direbana shi ma ya yi kokarin wuce motar shi kenan sai muka ji harbi ta ko ina," in ji Farfesa Ango.

Duk da cewa Farfesa Anogo na daya daga cikin dattawan arewan da suke sukar gwamnatin Nigeria mai ci yanzu, ya kore zargin cewa hakan na da nasaba da matsayinsa a siyasa.

Wasu bayanai na cewa motar sojojin ta fito ne daga jihar Kaduna, zuwa yankin arewa maso gabashin kasar da ake fama da rikicin Boko Haram.

Har yanzu dai ba a ji ta bakin hukumomin soji a kan kamarin ba, amma wasu bayanai na cewa tuni rundunar sojin jihar Bauchi ta sanar da hedikwatar tsaro a Abuja.