Yunkurin samar da ilimi ga yara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gordon Brown ya ce an kai hare-hare a kan dubban makarantu.

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani shiri wanda za a tara miliyoyin kudi domin ba da ilimi ga yaran da ke kasashen da ke fama da yaki.

Manzon musamman na Majalisar, Gordon Brown, ya fara ne da bukatar samar da kudin da za ta tallafa wa yara 'yan kasar Syria fiye da rabin miliyan da ke gudun hijira a Lebanon.

Tsohon Firai Ministan na Biritaniya ya ce an kai hare-hare a kan dubban makarantu a cikin shekaru biyar da suka wuce a kasashe irinsu Iraki, da Pakistan, Najeriya da Sudan ta Kudu.

Ya kuma ce za a kulla sabuwar yarjejeniya domin amfani da hanyoyin sadarwa na zamani don inganta tsaro a makarantu.