Yingluck za ta fuskanci tuhuma

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption yingluck shinawatra zata fuskanci shari'a

Kotun Kolin Thailand ta bukaci tsohuwar Firai Ministar kasar, Yingluck Shinawatra ta gurfana a gabanta domin amsa tuhuma kan zarge-zargen da ke da alaka da cin hanci da rashawa.

Ana zargin ta ne dangane badakalar sayar da shinkafa cikin farashi mai rahusa.

Kotun ta ce za a fara shari'ar ne a watan Mayu.

Wannan shi ne yunkuri na baya bayan nan na ganin an tuhumi Ms Yingluck, wacce tsige daga kan mulki a watan Janairu.

Ana zargin ta ne da laifin sakaci game da sayar wa manoma shinkafar cikin farashi mai rahusa, lamarin da ya sa kasar ta yi asarar biliyoyin daloli.

Idan aka same ta da laifin za ta iya shan daurin kimanin shekara goma a gidan kaso.