Akwai gyara a yakin neman zaben Buhari — Atiku

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Atiku Abubakar bai gamsu da tafiyar yakin neman Buhari ba

Tsohon mataimakin Shugaban Nigeria Alhaji Atiku Abubakar ya ce akwai kura kurai dangane da tsarin da ake bi na yakin neman zaben Janaral Buhari.

Amma ya ce "muna kokari mu gyara"

Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya shaidawa Darakatan yakin neman zaben Buhari, Rotimi Amaechi cewa duk abin da ake yi idan ba a gayyace shi ba, to ba zai je ba.

Tsohon mataimakin shugaban Nigeriar ya bayyana cewa shi babban dan siyasa ne, domin kuwa ya yi siyasa da 'Yardau da kuma Obasanjo, yana mai cewa domin haka bai kamata a ki sanya shi cikin yakin neman zaben ba.

Atiku Abubakar ya kuma musanta rahotannin da ke cewa zai koma jam'iyyar PDP.