'Yan matan Chibok na dajin Sambisa — Jonathan

Hakkin mallakar hoto

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya shaida wa BBC cewa yana sa rai za a kwato dukkan yankunan da Boko Haram ke rike da su a cikin wata guda.

Mr Jonathan ya ce, " Su ['yan Boko Haram] karfinsu na karewa a kulli yaumin."

Sai dai ya amince cewa jami'an tsaron kasar sun ja-kafa a yunkurin da suke yi na hana kungiyar ta Boko Haram fadada yankunan da take kwace wa.

Rundunar sojin kasar ta kwato yankuna da dama daga hannun 'yan Boko Haram.

Hare-haren da kungiyar ke kai wa dai sun yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 15,500 tun daga shekarar 2012.

'Yan matan Chibok suna nan da ransu

A hira ta musamman da BBC ta yi da shugaba Jonathan a Abuja, babban birnin kasar, ya kara da cewa: "Ina matukar fatan cewa ba za mu wuce wata guda ba za mu kwato dukkan garuruwan da Boko Haram ke rike da su."

Mr Jonathan ya ce 'yan matan Chibok na nan a raye, yana mai cewa za su bakin kokarinsu wajen kwato su daga inda ake tsare da su.

A cewarsa, da farko gwamnatin kasar ta raina karfin da 'yan kungiyar ta Boko Haram ke da shi, yana mai cewa rashin makamai ya taimaka wajen jan-kafar da aka yi a yunkurin kawar da su.