Nukiliya:Kerry zai yi bayani kan Iran

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Kerry bai jima da kammala tattaunar neman cimma yarjejeniya da Iran ba

Yayin da ya rage kwanaki goma a kai wa'adin da aka diba na cimma yarjejeniya a kan shirin nukiliyar Iran, sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, zai yi wa takwarorinsa na Birtaniya da Faransa da Jamus bayani ranar Asabar, a London.

Jami'an da suka halarci tattaunawar a Switzerland, sun ce har yanzu akwai muhimman bambance-bambance da ba a shawo kansu ba.

Shugaba Obama ya yi wani sakon hoton bidiyo ga shugabanni da kuma al'ummar Iran yana shawartarsu da su yi amfani da damar da aka samu a yanzu ta kulla kyakkyawar dangantaka.

Ya ce, ''a wannan shekara mun samu kyakkyawar damar da a shekaru da dama ba a samu ba domin kulla dangatanka ta daban tsakanin kasashenmu.''

To sai dai kuma ministan harkokin waje na Iran Jawad Zarif ya ce, lokaci ne da Amurka da kawayenta za su zaba tsakanin matsawa kasarsa da kuma cimma yarjejeniya.