An hallaka mutane 46 a Masallaci a Yemen

Image caption An zaman dar-dar a Yemen

Rahotanni sun ce an hallaka mutane da dama a hare-hare bama-bamai na kunar bakin wake Sanaa babban birnin Yemen.

An ta da bama-bamanne a Masallatai biyu lokacin sallar Juma'a.

Bayanai sun ce an hallaka mutane akalla 46 a masallacin Badr da kuma na al-Hashoosh.

Masu aiko da rahotanni sun ce Masallatan biyu na 'yan Shi'a ne da ake kira Houthis wadanda suka kwace iko da babban birnin a watannin da suka wuce.

An dade ana zaman dar-dar a kasar Yemen tsakanin al'ummomin kasar musamman da mayakan Al-Ka'ida wadanda ke kudancin kasar.