Ma'aikatan Nigeria na korafi kan albashi

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya, ma'aikatan gwamnati a jihohi da dama na kasar na korafin cewa ba'a biyan su albashi akan kari.

Ma'aikatan sun ce yanzu haka suna bin basussukan kudin albashi na watanni da dama.

To sai dai gwamnatocin jihohin na ikirarin cewa suna fama da karancin kudade ne sakamakon faduwar farashin man fetur.

Rahotanni sun ce jihohi da dama sun kasa biyan albashin ma'aikatansu da wasu watanni -- abin da ya jefa ma'aikatan cikin kuncin rayuwa.

Kungiyoyin kwadago na zargin gwamnatocin jihohin da karkatar da kudaden da suke samu ga harkokin siyasa gabannin zabukan dake tafe.

A jihar Binuwai, ma'aikatan na bin bashin kamar watanni hudu. A jihar Bauchi kuwa ma'aikatan na bin bashin albashin wata daya.

Amma gwamnati ta ce za ta kasa bashin zuwa kashi goma, yadda za ta rika biyan kashi daya a kowane wata na tsawon watanni goma kafin ta kammala.

A jihar Filato kuwa ma'aikatan na bin bashin watanni da dama.

Comrade Jibrin Kamga Banchir, shugaban kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Filaton, ya ce ma'aikatan jihar na bin gwamnati bashin albashi na watanni biyar.

Malaman makarantun firamare a jihar ta Filato na bin bashin albashin akalla watanni takwas, amma dai rahotanni na cewa yanzu gwamnati ta fara biyan basusukan malaman.

Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Filaton, Mista Ezekiel Dalyop, ya ce karancin kudade shiga daga baitulmalin tarayya da kuma kudaden shiga na cikin gida a jihar ne suka yi tarnaki ga biyan albashin ma'aikatan akan kari, amma ya ce suna kan kokarin magance matsalar.

Karin bayani