Obama ya soki Fraiminista Netanyahu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Obama ya yi sukan ne a wata hira da Huffington Post

Shugaba Obama ya zargi Fraiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da sa a dauka cewa abu ne da ba zai taba yuwuwa ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Palasdinawa.

Wannan shi ne kalaminsa na bainar jama'a na farko tun bayan da Mr Netanyahu, ya yi nasara a zaben da aka yi ranar Talatar da ta gabata.

Shugaba Obama, ya ce Amurka, ta cigaba da yin amanna cewa, samar da kasashe biyu na Isra'ila da Palasdinu, ita ce hanya daya tilo ta tabbatar da tsaro da zaman lafiyar Isra'ila.

Mr Obama ya soki, kalaman ranar zabe na Netanyahu, inda Fraiministan ya yi gargadin cewa tururuwar da Larabawa ke yi zuwa kada kuri'a, suna yi ne domin adawa da muradin Isra'ila.