Dakarun Chadi sun kashe 'yan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP

Jiragen sama masu saukar ungulu na Chadi sun yi lugude wuta a kan wasu sansanonin 'yan Boko Haram na Najeriya, inda suka kashe da dama daga cikin su.

Sojojin Nijer sun ce an kai harin ne a kusa da wani kauye a kan iyakar Najeriya da Nijer.

Dakarun Chadi da Nijer suna yakar 'yan Boko Haram ne a shirin hadin-gwiwa na kasashen, wadanda suka hada da Najeriya da kuma Kamaru.

Farmakin da sojojin suka kaddamar dai ya yi nasarar fatattakar 'yan Boko Haram daga garuruwa da dama da kuma gundumomin da suka karbe da farko a Najeriya.

Hakan na zuwa ne yayin da Najeriyar ke shirin gudanar da zabe a ranar Asabar mai zuwa.

Karin bayani