IS ta yi shirin kashe Sojojin Amurka

Mayakan Kungiyar Islamic State Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mayakan Kungiyar Islamic State

Hukumar sojin Amurka ta ce tana sanar da sojojin kasar maza da mata kusan su dari daya da aka ware domin halaka su a wani shafin intanet na wata kungiya da alamu ke nunawa tana da alaka da masu da'awar kafa daular Musulunci, IS.

Kungiyar wadda kafin yanzu ba a santa ba, wadda ke kiran kanta Islamic State Hacking Division, ta bukaci masu marawa IS baya da su kashe sojojin, da ta sa sunayensu da hotunansu da kuma wuraren da suke a shafin na intanet, bisa zargin cewa suna cikin aikin kai hare hare ta sama a kan mayakan IS a Iraq da Syria.

Sai dai sashen binciken miyagun laifuka na rundunar sojin ruwa ta Amurka, ya ce ba a tantance barazanar ba.

Ta kuma ce an shawarci sojoji da su san iya bayanan da za su rika bayarwa a game da kansu ta intanet.

Karin bayani