Kwalara ta kama mutane 20,000 a Ghana

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cutar kwalara na sa ruwan jikin mutum ya kare cikin sauri

Fiye da mutane 20,000 ne suka kamu da cutar kwalara a yankin Accra na kasar Ghana a cikin watanni takwas.

Haka zalika cutar ta yi ajalin mutane 120 daga watan Yunin 2014 zuwa watan Fabairun 2015.

Likitoci a kasar sun bayyana cutar da cewa ita ce annoba mafi girma da aka samu a tarihin kasar.

Rashin tsabtar muhalli da na ruwan sha ne ake zaton ya haddasa barkewar cutar a yankin.

Wasu daga cikin matakan da gwamnatin kasar ta dauka sun hada da wayar wa da jama'a kai game da tsabtace muhalli.

Haka kuma an ware rana ta musamman don tsabtace muhalli a yankin.