Yunkurin hana ta'addanci a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto .

A ranar Litinin ne Sakatariyar cikin gidan Biritaniya, Theresa May, za ta bayar da shawarwari a kan yadda za a magance ta'addanci, da kuma masu furta kalamai da ke rura wutar ta'addancin.

Mrs May za ta bayar da sanarwar da ke cewa akwai mutane kalilan da ke zaune a Biritaniya wadanda ke kyamar ala'adun turawa irinsu dimokradiyya da daidaito tsakanin al'umma.

A cewarta dole a tunkari irin wadannan mutane.

Mrs May za ta kara da cewa akwai bambanci tsakanin masu bin addinin musulunci -- kuma a ganin ta ala'adarsu ta zo kusan daya da ta Biritaniya -- da kuma masu tsattsauran ra'ayin da ke ganin ba zai taba yiwuwa musulmin kwarai ya zama mai bin ala'adar Biritaniya ba.