"Isra'ila ta keta dokokin yaki"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar dinkin duniya tana zargin Isra'ila da shiga hakkin Palestinawa a yakin bara.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoto a kan cewar Israela ba ta bi doka ba a kisan da ta yi wa Palastinawa, a lokacin yaki da suka yi a bara.

Dokar kasashen duniya dai ta hana kisan yara, da tsofaffi da kuma mata a lokacin yaki.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana haka ne a cikin wani rahoto da kwamitinta na kare hakkin bil adama zai gabatar a Geneva.

Rahoton ya yi bayani ne a kan yara akalla 400, 000 da suka raunana a lokacin yakin, wadanda kuma ke bukatar taimako, da kuma ci gaba da mamayar da Isra'ila ke yi wa yankin Palastinawa.

Isra'ila dai ta musanta wannan zargi.