Kenya za ta gina badala a kan iyakarta da Somalia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kenya zata gina badala a kan iyakar ta da Somalia.

Ministan tsaron Kenya, Joseph Nkaisery, ya ce za su gina badalar da za ta hana mayakan kungiyar Al Shabab kai hare-hare cikin kasar.

A cewarsa, za a soma ginin badalar ne a makon gobe, kuma idan an kammala ta, za ta raba garin Mandera na arewa maso kudancin Kenya, da na Bulahawa na Somalia.

Sai dai ana nuna damuwar cewa badalar ba za ta iya magance matsalar tsaro a yankin ba, kuma hakan zai kawo cikas ga harkokin cinikayya.

'Yan kungiyar ta Al-Shabaab dai sun dade suna kai hare-hare a kasar ta Kenya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.