Zabe ne zai kawar da Boko Haram — Obama

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Obama ya ce ya kamata a ceto 'yan matan da aka sace.

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya bukaci 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwarsu su yi zabe, yana mai cewa hakan ne kawai zai sa a kawar da Boko Haram.

A wani sakon bidiyo da ya aike wa 'yan kasar ta Najeriya, Mr Obama ya ce, "Boko Haram 'yan ta'adda ne da suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, don haka dole a kawar da su. Ya kamata a ceto yaran da suka sace. Kazalika ya kamata a dawo da mutane da rikicin ya kora daga gidajensu. Boko Haram na son wargaza Najeriya. Ta hanyar kada kuri'unku ne za ku tsare ci gaban kasarku".

Ya kara da cewa, "Najeriya kasa ce mai girma, ya kamata 'yan kasar su yi alfahari da ci gaban da suka samu. Kun samu 'yancin kai, kun kawar da mulkin soji kana kuka rungumi dimokradiyya, don haka yanzu kun samu damar sake gina kasarku ta hanyar yin zabe."

Mr Obama ya yi kira ga 'yan siyasa su hana magoya bayansu tayar da rikici.

Shugaban na Amurka ya ce dole a yi zabe cikin gaskiya da adali idan dai ana so mulkin dimokradiyya ya dore a kasar.