Senegal: Kotu ta daure Karim Wade

Image caption An zargi Karim Wade da azurta kansa ba bisa ka'ida ba.

A ranar Litinin ne wata kotu a Senegal ta yanke wa Karim Wade, dan tsohon shugaban kasar, Abdoulaye Wade hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari.

Kotun ta daure shi ne bayan ta same shi da laifin azurta kansa ta hanyar da ba ta dace ba a zamanin mulkin mahaifinsa.

Kazalika kotun ta nemi ya biya tarar sama da dala miliyan dari biyu.

A karshen makon jiya ne jam'iyyar adawa ta zabe shi a matsayin dan takararta na shugaban kasa.