An kori manyan 'yan sanda a Tunisia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mr Essid ya ce 'yan sanda sun yi sakaci da aiki.

Firai ministan Tunisia Habib Essid ya kori wasu manyan jami'an 'yan sandan kasar bayan mummunan harin da aka kai a wurin ajiye kayan tarihi da ke Bardo.

Wani mai magana da yawun Mr Essid ya ce ya lura da sakaci da dama ta fannin tsaro a lokacin da ya ziyarci gidan tarihin.

Mutane fiye da shirin ne suka rasa rayukansu, galibinsu 'yan yawon bude idanu daga kasashen waje.

'Yan sanda sun kashe biyu daga cikin 'yan bindigar da suka kai harin.

Tuni dai kungiyar IS mai ikrarin Jihadi ta dauki alhakin kai harin.