An kama wasu kan satar na'urar zabe a Zamfara

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Za a yi zaben shugaban kasa da 'yan majlisar dokoki na kasa a ranar Asabar mai zuwa

'Yan sanda a Niajeriya sun kama wasu mutane da ake zargi da hannu wajen bacewar na'urar tantance masu zabe a jihar Zamfara.

Kakakin 'yan sanda a jihar ya ce an sace na'urar ce a makon jiya a garin Anka da ke Jihar.

Na'urar dai ta bace ne a lokacin da ake horar da ma'aikatan zabe na wucin-gadi a garin.

Wasu jam'iyyun siyasa da kuma daidaikum jama'a a Najeriyar na nuna adawa da yin amfani da na'urar a lokacin zabe mai zuwa.

Hukumar zaben kasar, INEC ta ce amfani da na'urar wajen tantance masu zabe zai rage magudin zabe.