'Yan bindiga sun kashe mutum 13 a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption 'Yan ta'adda sun kai wa fasinjojin bus hari

Hukumar gabashin Afghanistan ta ce 'yan bindiga sun kashe fasinjojin bus goma sha uku, yayin da mutane biyu suka jikkata a wani hari da suka kai musu.

Lamarin ya faru ne da tsakar dare ranar Litinin a garin Wardak.

Har yanzu dai ba a tabbatar da ko su waye su ka kai wannan hari ba.

Kungiyar 'yan ta'addar Taliban da ke mulkin wasu sansanonin garin, sun yi Allah-wadai da kisan.

Da ma dai ana samun rahotannin hare-haren 'yan ta'adda a garin Wardak da garuruwa da suke makwabtaka da shi.