Limamai sun yi tur da kashe mace a Afghanistan

Image caption An yi zanga-zanga a Afghanistan a kan kisan Farkhunda

Kungiyar manyan Limamai masu fada a ji a kasar Aghanistan, ta yi Allah-wadai da rajamun da aka yi wa wata mata a garin Kabul a makon daya gabata.

Kungiyar ta ce matar mai suna Farkhunda, musulma ce ta kwarai , kuma ta yi gaskiya da ta kyamaci sayar da kayan tsubbu.

An kashe Farkhunda ne a wani gidan tsafi, yayin da ta ke zargin wani boka da sayarda kayan tsafe-tsafen.

Dubban mutane sun fito sun yi zanga- zanga , suna nema mata hakki a kan wadanda suka kashe ta, da kuma wadanda suka rura wutar kisan.

Tunda farko, an sallami kakakin 'yan sandan Kabul, saboda nuna goyon baya da ya yi a shafin Facebook a kan kashe matar.

A yanzu haka an dakatar da 'yan sanda 13 ana yi musu tambayoyi a kan batun.